Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Rage Farashin Man Fetur A Najeriya


Gwamnatin Taraiyar najeriya ta bayar da sanarwar rage farashin man fetur, wanda ya kawo karshen karin farashin da gwamnatin Obasanjo tayi a daidai lokacin da zata mika wa sabuwar gwamnati mulki.

A wata sanarwa da kakakin Gwamnatin Mr. Olusegun Adeniyi ya bayar, yace an cimma yarjejniyar rage farashin ne a wajen wani taro tsakanin wakilan Gwamnatin Taraiya da na kungiyar kwadago ta kasa. Sanarwar tace za a rage Naira biyar a farashin man, daga naira 75, sannan an jingine karin harajin VAT da gwamnatin Obasanjon tayi a jajiberen saukarta daga mulki.

Kazalika, gwamnatin ta yarda ta yiwa ma’aikatan kasar karin albashi da kashi 15 bisa dari, ta kuma nemi ma’aikata su tattauna kai tsaye da Hukumar Gwanjon Kadarorin Gwamnati, kan adawarsu da cefanar da Kamfanonin tatar man fetur na Kadauna da Fatakwal da aka yi.

Kungiyar kwdago, wadda a da ta aiyana gobe laraba ta kasance ranar da za a fara yajin aikin gama gari, tace zata tattauna wannan tayi na gwamnatin taraiya a yau, bayan nan kuma ta fito da matsayin karshe. Kafin cimma wannan yarjejniya dai, da har kungiyar kwadagon ta umarci ma’aikatan kasar da su fara yajin aiki daga gobe laraba, tunda yarjejeniya ta ci tura.

XS
SM
MD
LG