Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Yi Taron Kolin Tarayyar Afirka Makon Gobe Qaddafi Yana Shirin Tazarce A Shugabancin Kungiyar


Bisa ga tsarin karba-karba, shugabancin kungiyar hada kan kasashen Afirta ta AU zai koma hannun shugaban kasar Malawi dake kudancin Afirka ne, amma ga dukkan alamu za’a hadu da tangardar wajen kwace goriba daga hannun kuturu, domin masu fashin bakin siyasar Afirka na ganin zai yi wahala shugaba Qaddafin Libya dake rike da matsayin a yanzu, ya mika shi ga wani.

Jami’an Jakadancin kasa da kasa wadanda suka amince su tofa albarkacin bakinsu ba tare da bayyana sunayensu kafin taron kolin nahiyar Afirka mako mai zuwa, sun ce idan aka tuna da kumbiya-kumbiyar da Gaddafi yayi a taron kolin baya, lokacin da aka sauya wurin taron kolin daga Madagascar zuwa wani wajen saboda juyin mulkin da soja suka aiwatar.

A jawabin da ya yiwa manema labarai jiya litinin, babban Magatakardar kungiyar AU jakada Jean Mfasoni, yace koda yake bai kamata a yanzu ya bayyana cancantar Malawi ko rashin cancantar, amma yayi Karin haske.Mfasoni yana mai cewa ai batun wanda zai kama ragamar shugaban kungiyar, batu ne dake hannun wakilan kungiyar, kuma Malawi ce kungiyar tattalin arzikin kudancin Afirka SADC ta mika sunanta domin zama takarar shugabancin kungiyar tarayyar Afirka ta AU, fatan mu shinetaron kolin ya amince da hakan.

XS
SM
MD
LG