Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau ake sa ran yin muhawarar farko tsakanin ‘yan takarar shugabancin Amurka Barack Obama,da abokin karawar sa na Republican John  McCain


Yau ake sa ran yin muhawarar farko tsakanin 'yan takarar shugabancin Amurka Barack Obama,da abokin karawar sa na Republican John McCain,bayan da shi McCain ya jingine yakin neman zaben sa.

Wakilan Democrats suna zargin John McCain da laifin rugujewar yarjejeniyar dala bilyan dari bakwai na ceto cibiyoyin kudi,bayan shawarwari da akayi a fadar White House jiya Alhamis. Senata Chris Dodd,shugaban kwamitin harkokin Bankuna a majalisar Dattijai,yace taron 'Shirin ceto John Mccain ne".

Shi ma Obama ya zargi McCain da cusa siyasar yakin neman shugabancin Amurka cikin shawarwarin ceto cibiyoyin kudin.

XS
SM
MD
LG