Shugabannin
siyasar Zimbabwe sun shiga yini na biyu na shawarwari da nufin ceto shirin
daunin iko da aka cimma cikin watan jiya.
Tsohon
shugaban Africa Ta kudu Thabo Mbeki har yanzu shi yake shiga tsakani a
shawarwari tsakanin shugaba Robert Mugabe, da madugun 'yan hamayya Morgan
Tsvangirai, a fadar kasar, Harare.
Ahalin
yanzu kuma wani fitaccen dan siyasa Africa Wani fitaccen dan siyasa Africa Ta
Kudu kuma ya fita daga Jam'iyyar ANC, wannan alamace dake ci gaba da nuna rarrabuwa a Jam'iyyar.
Mbhamzima
Shilowa,tsohon Premier lardin Gauteng,ya gayawa manema labaru jiya Talata cewa
zai hade da bijirarrun 'yan Jam'iyyar ANC dake shirin kafa wata sabuwar
Jam'iyya. Shilowa yace bijirarrun zasu
yi taron kasa na sabuwar Jam'iyyar ranar 2 ga watan gobe a wuri da za a bayyana
nan gaba.
Shilowa
yana cikin magoya bayan Jam'iyyar ANC da suka ajiye aiki cikin watan
nan,bayanda Jam'iyyar ta tilastawa shugaban kasar Thabo Mbeki yayi murabus.
Bijirarrun
suna karkashin jagorancin tsohon ministan tsaro Mosiuoa Lekota,wadda yayi zargi
shugabannin Jam'iyyar da iza wutar kabilanci da kuma juyawa akidojin
Demokuradiyya baya. ANC ce take mulkin kasar tun kawo karshen mulkin nuna wariya
a 1994.