Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Iyaye Na Mika 'Ya'yansu Don Kunar Bakin Wake - Inji Kukasheka


 Kakakin Rundunar Sojin Najeriya Kanar Sani Usman Kukasheka
Kakakin Rundunar Sojin Najeriya Kanar Sani Usman Kukasheka

A hirarsa da Muryar Amurka kakakin sojojin Najeriya ya tabbatar wasu iyaye a yankin arewa maso gabashin Najeriya na mika wa kungiyar Boko Haram 'ya'yansu domin su shiga aiwatar da harin kunar bakin wake

A hirar da yayi da Muryar Amurka Kakakin sojojin Najeriya Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka ya ce wasu iyaye a shiyar arewa maso gabashin kasar na mika 'ya'yansu ga kungiyar Boko Haram domin yin anfani dasu a kunar bakin wake.

Yana mai cewa an sami wasu iyaye da suke ganin mika 'ya'yansu da suka haifa wata hanya ce ta taimakawa aikin Boko Haram na masha'a. 'Yan ta'addan sai su hure ma 'ya'yan nasu kunne har su kai ga aikin kunar bakin wake.

Masanin kimiyar zamantakewar jama'a Farfasa Muhammad Tukur Baba Iyan Mutum Biyu wanda yanzu yake bincike mai zurfi na sabon salon anfani da yara da kungiyar Boko Haram ke yi ya yi bayani kadan daga cikin abubuwan dake jawo hakan.

A cewarsa, na daya idan mutum ya yi imani da wata akida babu abun da ba zai iya yi ba a kanta. Na biyu irin sakon da 'yan ta'adan ke bada wa yana shiga cikin kunnen mutane musamman idan ana yinsa yau da kullum har ya shiga mutum. Wani abun kuma shi ne yin imani da abun da ba daidai ba saboda sabo da dadewa dashi. Wadannan abubuwan sukan sa mutane su yi imani da abun da ba haka yake ba.

Farfasa Tukur Baba ya bada shawara akan abun da yakamata a yi. Akwai hanyoyin shawo kan ta'addanci. Gwamnati zata yi nata. Shugabanni zasu yi nasu kana jama'a ma zasu yi nasu.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG