Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jihar Neja Wasu Sun Kai Karar Wanda Ya Danne Masu Nera Miliyan Dari


Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja
Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja

Mutane da yawansu ya kai dari sun shigar da karar Muhammed Ibn Indaba shugaban kamfanin Lalle Travel Agency dake aikin kai alhazai zuwa yin aikin hajji domin sauke farali

Masu karar suna neman kotun da ta karbo masu kudadensu sama da nera miliyan dari da suka baiwa mutumin tun shakarar 2011 domin ya kaisu aikin hajji.

Kawo yanzu da suka shigar da karar Muhammed Ibn Indaba bai kaisu aikin hajjin ba kuma bai mayar masu da kudadaensu ba.

Lauyan mutanen Muhammed Bara'u Shehu Kagara yace shekaru uku da suka gabata mutane sun tara kudi suka biya kamfaninsa da niyyar cewa zasu je kasa mai tsarki su sauke farali. Amma hakan bai yi ba. An bishi da lallashi an rubuta masa wasiku ya biya kudin. Bai biya ba ya ki. Dalili ke nan da suka shigar da kara kotu ta biya masu bukata.

Masu shigar da karar sun yi cincirindo a harabar kotun. Wani Alhaji Isa Makwa yace shekaru hudu da suka wuce ya tara kudaden mutane 35 ya biya kamfanin domin zuwa hajji. Babu wanda ya samu zuwa cikinsu. Wani yace sun kai mutumin har EFCC an dauki jawabi an kaishi kotu amma sai labarai.

Amma shi Muhammed Ibn Indaba yace kudaden basa hannunsa duk da cewa ya tabbatar da lamarin. Yace kudaden suna wurare daban daban har ma da kasa mai tsarki.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG