Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A karon farko a Amurka hoton bakar fata Tubman zai fita kan takardar dala 20


Harriet Tubman wadda hotonta zai fita a takardar kudi dala 20

Bakar fatar nan Ba’amurkiya mai adawa da rashin mutunta bil’adama, wacce kuma ta jagoranci daruruwan jama’a wajen neman ‘yantarwa daga bauta, wato Harriet Tubman, hotonta zai maye gurbin hoton Andrew Jackson akan takardar Dala 20 ta kudin Amurka.

A jiya Laraba Jack Lew Sakataren baitul malin Amurka ya tabbatar da haka, tare da cewa, Tubman ce bakar fatar da zata zama ta farko daza’a sa hotonta kan takardar kudin Amurka cikin tsawon shekarufiye da 100.

Sakataren baitul malin bai fadi lokacin da za a fara ganin wannan sabuwar takardar kudin a hannun jama’a ba. A baya dai ya so a lika matar ne a takarda Dala 10 a watan Yunin da ya gabata, amma ya sake tunani zuwa kan Dala 20 sakamakon matsin lambar kungiyoyi da daidaikun mutane.

Andrew Jackson, tsohon shugaban Amurka ne akan takardar Dala 20 din, wanda kuma shine ummal uba’isin dokar nan ta kauda Indiyawan dajin Amurka a shekarar 1830, wacce ta tursasa kaurar da ta yi sanadiyyar mutuywar dimbin ainihin ‘yan asalin Amurka.

An haifi Tubman mai suna Araminta Ross ne a shekarar 1822, ta kuma taso ne a cikin bauta a gabashin jihar Maryland. Masana tarihi sun bayyana cewa an rabata da iyayenta tana shekaru 6 aka bautar da ita, sannan ta sha mugun duka tana shekaru 12 wanda ya haifar mata da yawan suma tsawon rayuwarta.

XS
SM
MD
LG