Gwamantin neman hadin kan kasar ta bawa jami’an tsaro damar ci gaba da aikinsu na tsare gwamantin kasar, sannan kuma tace za a dora duk wani laifin rashin biyayya ga tsarin da zai kawo tsaron da aka yi akan sabuwar gwamantin hadakar.
Sanarwa kuma ta bayyana cewa, wannan matakin da aka dauka abu ne da ya shafi kasar, wanda ba ma a bukatar wani ya sa baki daga ketare. Gwamantin ta Tripoli dai tace suna nan sun maida hankali don ci gaban zaman lafiya don kaucewa zubar da jinni.
Ya zuwa yanzu dai, Majalisar Dinkin Duniya ba ta ce komai ba akan lamarin, duk kuwa da cewa itace ta tsara wannan shirin na kawo gwamantin hadakar ta Libya don kawo karshen tashin hankalin da aka sha fama da shi a tsakanin darewar gwamantocin biyu.