Tsohon mai baiwa shugaban Amurka shawara akan sha’anin tsaro John Bolton, a jiya Litinin ya ce zai bayyana domin ba da shaida a zaman sauraren karar tsige shugaba Donald Trump idan har majalisar dattawa ta gayyace shi, lamarin da zai baiwa Democrats karin haske kan ainihin abin da ya faru a bayan fage akan yunkurin Trump na tursasawa Ukrain gudanar da bincike da zai amfane shi a siyasance.
Bolton, wani mai akidar jaddada karfin ikon fada a ji da Amurka take da shi a duniya, yayi aiki a matsayin jami’in tsaro na 3 na Trump tsawon watanni 17 kafin a cire shi a watan Satumban da ya gabata, sakamakon takaddama akan yadda za’a tafiyar da dangantaka da Iran, Korea ta Arewa da Afghanistan.
A shirye-shiryen kada kuri’ar tsige Trump a majalisar wakilai, masu bincike sun ki gayyatar Bolton, saboda fargabar tsawaita zaman shari’a a kotu, akan ko za’a iya tilasta masa ba da shaida, ko kuma zai yi biyayya ga umarnin Trump da ya hana wa manyan jami’ai bayar da shaida.
A yayin da zaman sauraren karar ta tsige Trump ya koma a majalisar dattawa, duk da yake ba’a tsayar da ranar somawa ba, Bolton ya ce zai so ya warware wasu al’amura masu sarkakiya gwargwadon iyawar sa,cikin kyakkyawar natsuwa da kumanazari.