Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gurbataccen Abinci Ya Kwantarda Daruruwan 'Yan Gudun Hijira.


Wasu suke gudun rikicin da ake yi a Mosul

Kungiyar kula da ‘yan gudun hijira ta kasa da kasa ta bada rahoton cewar kimanin muatne 752 suka kamu da rashin lafiya.

Kungiyar kula da ‘yan gudun hijira ta kasa da kasa ta bada rahoton cewar kimanin muatne 752 suka kamu da rashin lafiya. Daga cikin wannan adadi mutum 312 aka kwantar a asibitotci, kana akalla wasu mutane biyu suka mutu da suka hada da wani yaro da wata mace sakamakon cin abincin daya lalace a wani sansanin da aka ajiye wadanda suka rasa gidajensu a wajen birnin Mosul na kasar Iraq.

Kakakin kungiyar ta kula da bakin hauren Joel Millman ya fada a shekaranijya Litinin cewar wani dan kwangila ne ya kawo abinci da misalign karfe hudu na rana don buden baki na watan Ramadana da suka saba yi da za a raba abincin a daidai karfe 7:30 na yamma.

Kakakin yace hukumomi na binciken lamarin don gano inda gurabataccen abinci ya fito ko kuma abinci ya gurbace ne tsakanin lokacin da aka kawo da lokacin da raba.

Bayan an basu abincin, mazauna sansanin sun ce mutane da dama sun kamu da ciwo kana kuma hukumomi basu da isasshen motocin kwasan marasa lafiya inda suka cika motocin bos suka makil da mutane.

Facebook Forum

Arewa A Yau

Arewa A Yau
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:47 0:00
XS
SM
MD
LG