Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Wadanda Suka Mutu A Harin Ankara Ya Karu


Wani mutum yake kuka kan gawar wani da harin ya rutsa da shi.

Adadin wadanda suka halaka sakamkon tagwayen bama-bamai da suka tashi a wani gangamin neman zaman lafiya a Ankara, babban birnin kasar, ya haura zuwa mutum 95, da wasu kusan metan kuma wadanda suka jikkata.

A daren jiya ne hukumomin kasar suka bada wannan karin bayani. Masu aiki a fannin kiwon lafiya sun ce sai tayu wannan adadi ya karu cikin kwanaki masu zuwa, domin ganin yadda wasu da jikatarsu tayi tsanani, sunan kwance rai hanun Allah.

Fashe fashen sun auku ne kusa da wata kofar fita daga tashar dogo dake gundumar Ulus a Ankara, watakil da zummar su haddasa mummunar hasarar rayuka tsakanin wadandan suka halarci gangamin, da kungiyoyin kwadago da kuma na fararen hula suka shirya.

An sami rudani da dimauta a inda aka kai harin, rahotanni suka ce gawarwaki ne suke zube ta ko ina da tufafi da tutoci ruwan dorowa alamar kungiyar masu ra'ayin kurdawa.

Masu fashin baki suna zaton wannan aikin kungiyar ISIS ne ko kuma wata kungiya mai kishin kasar wacce take adawa da kungiyar PKK da aka haramat a kasar. Babu wata kungiya da fito nan da nan ta dauki alhakin kai wannan hari.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG