'Yan Jihyar Adamawa su na tsallakawa zuwa wasu jihohi ko kuma cikin Kamaru don su iya yin wayar tarho. An tsinke layukan tarho a jihohin Adamawa da Borno da Yobe tun lokacin da aka kafa dokar-ta-baci wata gudan da ya shige.
Al'ummar Adamawa Su na Ketarawa Wasu Jihohi Domin Yin Waya
1
Wasu mutanen da suka baro Yola, babban birnin Jihar Adamawa, a kan babura domin kawai su samu damar yin waya sun tsaya a gefen hanya a Jihar Taraba su na lalubo 'yan'uwa da abokan arziki.
2
'Yan Jihar Adamawa dake tserewa zuwa jihohi makwabta domin yin waya, sun tsaya a gefen hanya inda zasu iya yin waya a jihar Taraba, kafin su sake komawa gida.
3
Wasu 'yan jihar Adamawa da suka taso takanas ta kano zuwa taraba domin yin waya sun samu wani wurin da zasu iya yin wayar a cikin daji a gefen hanya.
4
Wasu 'yan jihar Adamawa da suka taso takanas ta kano zuwa taraba domin yin waya sun samu wani wurin da zasu iya yin wayar a cikin daji a gefen hanya.