'Yan Jihyar Adamawa su na tsallakawa zuwa wasu jihohi ko kuma cikin Kamaru don su iya yin wayar tarho. An tsinke layukan tarho a jihohin Adamawa da Borno da Yobe tun lokacin da aka kafa dokar-ta-baci wata gudan da ya shige.
Al'ummar Adamawa Su na Ketarawa Wasu Jihohi Domin Yin Waya
5
Wata mace mai sayarda doya, wadda kasuwarta ta bude a wani kauyen jihar Taraba, saboda tana samun ciniki daga mutane masu zuwa kauyen yin waya daga Jihar Adamawa.
6
Wata motar soja dauke da sojojin da aka girka a Jihar Adamawa karkashin dokar-ta-baci
7
Wasu motoci biyu kan hanyar da kusan babu komai kanta a Jihar Adamawa, sun doshi wata makwabciyar jiha domin yin waya