Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GIRKA: Akwai Kwarin Gwiwa - inji Tsipras


[FILE]

A yau Laraba, Firai ministan kasar Girka, Alexis Tsipras, ya ce yana da kwarin gwiwar zai yi nasarar kawai ga gaci, game da wa’adin karshe da shugabannin nahiyar Turai suka saka mai, domin ganin ya ceto tattalin arzikin kasar nan da karshe makon nan.

A wani jawabi da ya yi, a gaban majalisar dokokin kasashen nahiyar ta turai, firai ministan, ya kuma kare dalilin da ya sa kasarsa ta ki amincewa da tsauraran sharuddan da aka gindaya mata domin neman mafita daga kangin da ta shiga.

Shugaban na Girka wanda wasu suka yiwa lale yayin da wasu suka mai Shewa a zauren majalisar, ya kara da cewa, duk wani mataki da za a dauka ya kamata ya zamnato na bai-daya, wanda zai samar da ayyukan yi ya kuma bunkasa harkokin cinikayya.

A yau Laraba, Girkan ta mika wani sabon kokon baranta na neman mafita ga matsalar tabarbarewa tattalin arzikinta, kamar yadda hukumar Gidauniyar dake ceto kasashen da ke amfani da kudin Euro na bai-daya ta tabbatar.

XS
SM
MD
LG