Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alhazan Najeriya 10 Sun Rasu A Saudiyya


Jagoran tawagar likitocin gwamnatin tarayya dake kula da Alhazan Najeriya a saudiyya Dr Ibrahim Kana, ya bayyana rasuwar Alhazan Najeriya kimanin su goma kafin hawan Arfa na hajjin bana.

Likitan wanda ke jawabi a lokacin taron da hukumar alhazan Najeriya da masu ruwa da tsaki a birnin makka ya yiwa wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Hassan Maina Kaina Karin bayanin cewa kwana uku da zuwa arfa ne Allah yayiwa Alhazan cikawa, guda biyu sun rasu a Madina, guda takwas kuma sun rasu ne a Makka, ya kuma kara da cewa bincike ya bayyana cewa Alhazan sun rasu ne a sakamakon rashin lafiya irin su ciwon hawan jini da kuma ciwon suga.

Da yake amsa tambayar da wakilin sashen Hausa ya yi akan canjin da aka samu daga shekarar data gabata, Likitan ya bayyana cewa an sami raguwar yawan Alhazan dake rasuwa, domin a cewar sa shekarar data gabata mutane ashirnne suka rasu a dai dai irin wannan lokaci.

Sai dai Dr Ibrahim Kana ya ce, akwai Alhazan Najeriya da dama da aka kwantar a asibiti amma yawanci an sallame su, dan haka a cewarsa lallai an sami ci gaba kwara idan aka kwatanta lamarin na bana da shekarar data gabata.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:04 0:00

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG