Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aljeriya Ta Dage Dokar Ta Baci Data Kafa Shekaru 19 Da Suka Wuce.


Daliban Aljeriya suke karawa da 'yansanda kusa da ma'aikatar ilmin kasar a Algiers.

Aljeriya ta dake dokar ta baci da ta kafa shekaru 19 da suka wuce, a wani yunkurin dadawa ‘yan hamayya domin kaucewa guguwar canji da take ratsa kasar larabawa.

Aljeriya ta dake dokar ta baci da ta kafa shekaru 19 da suka wuce, a wani yunkurin dadawa ‘yan hamayya domin kaucewa guguwar canji da take ratsa kasar larabawa da gudun kada guguwar ta hambare gwanatin shugaba Abdelazizi Bouteflika.

Jiya Alhamis ce aka wallafa dokar shugaban kasa da ta dage dokar ta bacin cikin kundin gwanati.

Kawo karshen dokar ta bacin yana daga cikin bukatu da ‘yan hamayya dake zanga zanga ko wani mako shigennwadanda aka yi a Tunisia da Masar, suka gabatar. An kafa dokar ta bacin ne domin baiwa hukumomi ikon shawo kan masu zazzafar ra’ayin Islama,amma cikin shekaru da suka wuce an sami lafawar tashe tashen hankula,shi ya sa ‘yan hamayya shiga zargin cewa ana amfani da dokar ce wajen take ‘yancin walwalar siyasa.

Shugaban Amurka Barack Obama ya marhabin da soke dokar,yace wan nan alamace mai kyau,duk da haka ya yi kira ga shugabannin kasar su daukin karin matakai biyan bukatun jama’arsu na basu karin ‘yanci.

XS
SM
MD
LG