Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa A Victoria Island Da Lekki A Birnin Legas


Ambaliyar Ruwa a Birnin Lagos

A kwashe makonni biyu ana kwarara ruwan sama a birnin Legas wanda ya yi sanadiyar ambaliyar da ya shafe titunan mota.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka kwashe kwanaki ana tafkawa a birnin Legas, ya haifar da ambaliya wanda yasa har Gwamnatin jihar ta um arci jama’a su tashi daga yankunan domin tsira da rayukan su.

Koda yake akasarin mazauna wadannan unguwanni dai masu hannu da shuni ne za a iya cewa wasu daga cikin su tuni suka fice daga gidajensu wasu kuma suka kama Otel Otel.

Ambaliyar Ruwa a Birnin Lagos
Ambaliyar Ruwa a Birnin Lagos

Gwamnatin jihar Legas tuni ta yi gargadin cewa mutane su fice daga unguwar da aka iya samun ambaliyar ruwan abinda kuma yake ci gaba da haifar da fargaba a zukatan mazauna irin wadannan wurare.

Wasu dake wadannan unguwani dai sun bayana cewa alamarin sai dai wanda idon sa ya gani domin a cewar su mako biyu akayi ana kwarara ruwan sama,a birnin na Legas, iknda ma hanyar da ta taso daga Victoria Island zuwa Lekki mutun baya iya tantance kan hanyar domin ruwa ya shafe shi kamar babu titin mota ko kuma labbatu.

Titin da ambaliyar yafi shafa a unguwar Victoiria Island, ya hada da layin Adetokumbo Ademola, inda motoci haya da masu keke Napep, watau babur mai taya 3, suka dakatar da zirga zirga zuwa wadannan wurare tare kuma da kara farashin kudaden da suke karba ga wadanda suka yi kasadar shiga ruwan.

Wasu sun danganta ambaliyar da ake fuskanta a birnin Legas, akan gine gine da masu hannu da shuni ke yin a hanyoyin ruwa, inda ma wasu ke dora alhakin ambaliyar akan wani sabon tsibiri da ake ginawa mai suna “Eko Atlantic City”.

Tuni dai rundunar ‘yan Sandan jihar ta Legas ta gargadi masu motoci da su kauracewa hanyoyin dake fuskatar ambaliyar ruwan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG