Accessibility links

Ambaliyar ruwa ta yiwa kasar Pakistan barna

  • Jummai Ali

Wasu 'yan kasar Pakistan suke, ratsa hanyoyin wadanda ambaliyar ruwa ta lulube su a sakamakon ruwan sama sama kamar da bakin kwarya a birnin Karachi

Prime Ministan Pakistan Yousouf Reza Gilani yayi kira ga yan kasarsa da su hada kai su taimaki kasar ta farfado daga ruwan sama kamar da bakin kwarya data kashe fiye da mutane dari da arba’in kuma ambaliyar ruwa ta kanainaye fiye da hecta milyan daya da rabi na fili a yankunan kudancin kasar.

A jiya asabar da dare Mr Gilani yayi wannan roko a wani jawabi daya gabatar ta gidan talibijin na kasar, bayan da ruwan sama kamar ta bakin kwarya ta yiwa birnin Karachi barna, inda har aka kwantar da mutane da dama a asibiti.

Yace gwamnatin kasar tana fatar ware dala miliyan tamanin domin taimakon, wuraren da ambaliyar ruwa ta yiwa barna, to amma kuma ya nemi taimakon kasashen duniya.

Lardn Sindh ambaliyar ta fi yiwa barna. Gwamnati Pakistan tace gundumomi ashirin da biyu daga cikin gundumomin ashirin da uku na lardin Sindh da wasu yankunan lardin Baluchistan duk ambaliyar ruwa ta kanainaiye su. Rahotanin baya bayan nan sun baiyana cewa kimamin mutane dubu maitan sun bukatar tamakon gaggawa na jin kai nan da nan.

Jiya asabar Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar da sanarwar dake cewa bisa bukatar kasar Pakistan, Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da bada taimakon jin kai, ga wannan bala’i

XS
SM
MD
LG