Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AMSOSHIN TAMBAYOYINKU: *Tarihin Sani Dan Indo *Wane ne comrade (Kwamrad)?


Ibrahim K Garba

Tambaya Ta Daya

Assalama alaikum Sashin Hausa na Muryar Amurka. Don Allah ku yi min karin haske kan Kalmar Comrade.

Shin wane ne comrade?

Me kalmar comrade (kwamrad) ke nufi?

Shin wadanne alamomi comrade (kwamrad) ke da su?

Ta yaya aka samu wannan sunan; kuma a wace shekara?

Wai da gaske ne comrade (kwamrad) bai da aikin yi?

Masu tambayar kaka Mai Yidi; da Alh Bukar Gursuma Damasak, jijar Bornon Najeriya.

Tambaya Ta Biyu

Don Allah VOA Hausa, a ba ni dan takaitaccen tarihin shahararren mawakin Hausa dinnan, marigayi Sani Dan Indo, wanda ya matu a 2016.

Mai tambaya, Yusuf Abubakar Bauchi.

Za mu fara jin amsoshin tambayoyin su Kaka mai Yidi kan Comrade. Idan masu tambayar, da ma sauran masu sha’awar jin amsar, na tare da mu, wakilinmu a shiyyar Adamawa, Muhammad Salisu Lado, ya samo amsoshi daga Dr. Babikwai Girei na Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, jahar Adamawa, Najeriya.

Sai kuma amsar tambaya kan shahararren mawakin Hausa, Sani Dan Indo, wanda ya rasu a watan Fabrairu na 2016. Idan mai tambayar, Yusuf Abubakar Bauchi, na tare da mu, wani tsohon edita a Sashin Hausa, kuma mai matukar sha’awar wakokin Sani Dan indon, wato Mallam Shehu Yusuf Kura, ya ba da amsa.

A yi saurare lafiya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:13:07 0:00

XS
SM
MD
LG