Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AMURKA: Ana Zargin Wasu Mazauna Rasha da Satar Bayanai


Wani bangaren hedkwatar tsaron Amurka

Amurka na zargin wasu mazauna kasar Rasha da satar bayanai daga wasikun naurar kwamfuta ta babban shugaban hedkwatar hukumar tsaro ta Pentagon.

Kafofin yada labarai na kasar Amurka sun bayyana cewa wasu masu satan bayanai ta duniyar gizo da suke da mazauni a kasar Rasha sun samu nasarar kutsawa cikin runbum bayanai nan Email na babban shugaban hukumar tsaro ta Pentagon abinda yasa aka kulle wannan matattaran bayanan har na tsawon sati biyu.

Wadannan kafofin yada labarai sun ambato wani babban jamiin hukumar na taba tabbacin aukuwar wannan aika-aikan.

Kafar yada labarai ta NBC ce ta fara bararan wannan batu sai dai abinda bata tantance ba shine ko wannan aikin gwamnati ne ko kuma na wani mutun guda ko kuma gungun mutane.

Wannan harin dai ya faru tiun a ranar 25 ga watan jiya kuma ya shafi maaikatar hukumar har kusan su dubu 4, sai dai bayanan sun ce ba wani bayanai muhimmai da aka sace ko kuma aka yi wani abu dasu, amma dai maaikatar ta PENTAGON ta kulle wannan runbun na tattara bayanai lokacin da ake gudanar da bincike.

Wasu jami'an kasar Amurka sun bayyana kwanan nan cewa a cikin yan kwanakin da suka gabata kusan ma'aikatan Amurka miliya 21 akasamu kaiwa ga bayanan su ta runbun adana bayanai wanda ake tuhumar cewa daga kasar China ne wannan abu ya fito.

XS
SM
MD
LG