Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Koriya ta Arewa Sun Kammala Taronsu Da Alkawarin Kwance Makaman Zirin Koriya


Shugaba Kim Jong Un da Shugaba Donald Trump

Duk da cewa sun bar sauran duniya cikin duhu akan abun da suka cimma shugaban Amurka Trump da shugaban Koriya ta Arewa sun kammala taronsu da alkawarin kwance makaman zirin Koriya

Ganawa ta musamman da aka gudanar tsakanim shugabannin Amurka da na Koriyaa ta Arewa ya kawo karshe a jiya Talata tare da alkawarin kwance damarar makamai masu linzami a zirin Koriya.

To sai dai kuma abinda ake sa ran ya zama babban labari, ba shine ya fito fili ba a karshen yarjejeniyar da kasashen biyu suka sawa hannu.

Domin ko Shugaba Trump yaci gaba da nanata cewa zai dakatar da atisayin da sojojin Amurka ke yi da na Koriya ta Kudu a wani matakin kwantar da hankalin Kim Jong Un.

Wannan shawarar ta Trump dai ta bar kawayenAmurka da ma sauran jamian sojan Amurka a zirin dake bukatar Karin haske game da inda aka kwana.

Wannan matsayin na Trump dai ya bar kwararru a harkan soji da sanin rashin tabbas akan wannan batun.

Yanzu haka dai Koriya ta Kudu ta shiga tsaka mai wuya domin ko wannan shawarar shugaba Trump ta sata kasa gane shin ina aka dunfara ne, domin shi ma mai Magana da yawun Fadar Blue House ya ce akwai bukatar tantance abinda kalaman Shugaba Trump ke nufi,

Sai dai a wuri daya kuma ra’ayin ‘Yan majilisar dokokin Amurka ya banbanta akan wannan ganawar da aka yi tsakanin shugaban na Amurka da takwaran aikin sa na Korea ta Arewa.

Ganawar da shugabannin biyu suka yi a kasar Singapore ya zame wani abin tarihi, wanda aka kammala da alkawarin cewa kasar ta Koriya ta Arewa zata sukurkuta makaman ta dake zirin na Koriya ta Arewan.

Haka ita ma Amurka tace zata dakatar da atisayin da sojojin ta keyi da sojojin Koriya ta Kudu

Anan Washington dai da yawan ‘yan majilisar dokokin sunce suna ganin wannan ganawar ita ce matakin farko.

Amma kuma yayin da ‘yan jamiyyar Republican keda tabbaci ko kwarin gwUiwa akan wannan yarjejeniyar suko yan jamiyyar Democrat na cewa ne har yanzu da sauran rina a kaba domin ko yarjejeniyar an barta a dunkule ba a fayyace ainihin muhimman batutuwa ba a cikin wannan lamari.

Sai dai daga karshe kalaman na ‘yan majilisar ya bukaci kasashen biyu dasu samar da zaman lafiya mai dorewa a zirin na Koriya da kuma kyakkyawar dangantaka tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa, tare da ganin an sako Fursunonin nan da suka bata. Sai dai kuma kasashen biyu sun yi alkawarin bibiyar duk wasu yarjejeniyoyin da aka cimmawa.

To amma kuma yarjejeniyoyin basu basu shata wani tsari na sadidan ba game da kwance damarar makamin nukiliyar kasar ta Koriya ta Arewa.

Sanatan Jamiyyar Democrat, Sanata Bob Menendez ya ce wannan ita ce yarjejeniya mafi rauni da ya taba gani wanda aka kulla da Koriya ta Arewa, ya ce amma dai mun zura ido muga kuma ina aka dosa kuma wani muhimmin shiri aka tsara.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG