Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka da Philipines sun Kaddamar da Wani Atisayen Soji


Sojojin Amurka da Philippines.

Kasashen Philippines da Amurka sun kaddamar da wani atisayen soji na shekara-shekara a tekun Kudancin China.

Kasashen Philippines da Amurka sun kaddamar da wani atisayen soji na shekara-shekara a tekun Kudancin China, daura da ruwayen da China ke takaddamar mallakarsu da makwabtanta.

Sojojin ruwa wajen 5,000 daga kasashen biyu sun fara atisayen kwanaki 11 a yau dinnan Litini. Makasudin wannan atisayen na Philippines da ake kira "Phiblex," shi ne a gwada shirin kasashen biyu na iya tinkarar duk wata barazana ta bazata.

XS
SM
MD
LG