Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Bude Wani Sansanin Jiragen dake Sarafa Kansu a Kamaru


Samfarin jirgin dake sarafa kansa da kansa, wato baya bukatan matuki, irin wanda Amurka ta girke a arewacn Kamaru domin tara bayanan asiri a yaki da Boko Haram
Samfarin jirgin dake sarafa kansa da kansa, wato baya bukatan matuki, irin wanda Amurka ta girke a arewacn Kamaru domin tara bayanan asiri a yaki da Boko Haram

Amurka ta bude wani sansanin jirage mara matuka a arewacin Kamaru domin taimakawa a yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram a yankin Yammacin Afrika.

Yanzu haka Amurka na da adadin sansanin jirage mara matuka guda hudu a yankin Yammacin Afrika wadanda ta girke saboda yaki da kungiyar Boko Haram.

Uku daga cikinsu kuma na jamhuriyar Nijar da Burkina Faso da Chadi, wadanda suka mai da hankali kan mayakn Boko Haram da ke ta da kayar baya a Najeriya.

Sabon sansanin da aka bude kuwa yana kasar Kamaru ne, wacce ke makwabtaka da Najeriyar.

A cewar tsohon jakadan Amurka a Najeriya, John Campbell, a baya Najeriya, ba ta yi amfani da ayyukan tattara bayanan sirri da Amurkan ta sama mata ba.

YA CE “Akwai tayi da akawa gwamnatin Najeriya a lokacin da aka sace ‘yan matan Chibok, an kuma tura kwararrun daga kasar Amurka, amma hakan bai sa an kai ga gaci ba.”

Sai dai yayin da Boko Haram ta ji takura daga dakarun hadin gwiwa da aka kafa, a ‘yan makwannin da suka gabata, kungiyar ta zafafa hare-haren kunar bakin wake inda takan tura kanana yara mata zuwa masallatai da kasuwanni domin ta da bam a arewacin Najeriya.

Amma Robert Martin da ke rubutu a wata mujalla da ke sharhi kan harkar tsaro mai suna Janes Defence Weekly, wacce ake bugawa a duk mako, ya ce jirage mara matuka dake shawagi a sararin samaniyar Kamaru da Najeriya za su taimaka…..

“Idan ka kula, matsalar da Najeriya da makwabtanta ke fuskanta Ita ce rashin bayanan sirri a yakin da su ke yi da Boko Haram, hakan ya sa da dama daga cikin kokarin da su ke yi ba ya tasiri.”

A arewacin kasar ana samun karancin labarai da ke fitowa, hakan ya sa Campbell ya ce sojojin Najeriya a lokuta da daman ke ikrarin samun nasara.

“Hanyoyin samun labaranmu ba su da yawa, ba kuma a barin ‘yan jarida su je ko ina, hakan ya sa bamu da madogara illa abinda sojojin suka ce.”

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin kawo karshen kungiyar ta Boko Haram. Sai dai Martin yana ganin har yanzu ana jan kafa a yakin.

“An dade ana shirye shiryen tunkarar mayakan, amma Shugaba Buhari ya taka rawar gani da ya ciyar da yakin da ake yi da mayakan gaba, amma kuma duk da kudaden da ake sakawa akwai alamun jan kafa a lamarin. Shugaba Buhari ya saka wa’adin watan Disamba domin a kawo karshen ‘yan kungiyar, kamata ya yi a ce mun ga karin hare-hare ta yadda za a kawo karshen Boko Haram ta yadda za ta zamanto ba ta da tasiri”

Bisa ga dukkan alamu, wasu dama na ganin kamar zai wuya a cimma wa’adin watan Disamba da aka dibarwa dakarun, a matsayin lokacin da za a kawo karshen kungiyar ta Boko Haram.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG