Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Kafa Takunkumi Kan Dan Tsohon Shugaba Lansana Conte Na Guinea


A cikin wata wasikar da ya aikewa da majalisar dokoki, shugaba Obama yace Ousmane Conte na Guinea da Mohammed Bachir Sulaiman na Mozambique da kuma wasu mutanen su uku, sun cancanci a kakaba musu takunkumi a karkashin Dokar Madugan Safarar Kwayoyi ta Amurka.

Amurka ta kafa takunkumi a kan dan marigayi shugaba Lansana Conte na kasar Guinea, da kuma wani dan kasar Mozambique a bayan da shugaba Barack Obama ya ayyana su a zaman madugan kungiyoyin safarar muggan kwayoyi.

A cikin wata wasikar da ya aikewa da majalisar dokoki, shugaba Obama yace Ousmane Conte na kasar Guinea da kuma Mohammed Bachir Sulaiman na kasar Mozambique da kuma wasu mutanen su uku, sun cancanci a kakaba musu takunkumi a karkashin Dokar Madugan Safarar Kwayoyi ta Amurka.

Ousmane Conte, wanda mahaifinsa ya mulki kasar Guinea na shekaru masu yawa har zuwa rasuwarsa a 2008, ya furta da bakinsa a baya cewa yana da hannu a safarar muggan kwayoyi, amma ya musanta cewa shi madugun wata kungiyar safarar kwayoyin ne.

Wani babban jami’in ma’aikatar harkokin kudi ta Amurka yace Mohammed Bachir Sulaiman na kasar Mozambique babban madugun fataucin muggan kwayoyi ne, kuma kungiyarsa tana cikin wadanda suka kara karfin safarar muggan kwayoyi da batar da sawun kudaden haramun dake karuwa a fadin nahiyar Afirka.

An ayyana wasu kamfanoni uku na Sulaiman a zaman bangaren fataucin kwayoyin nasa. Wannan yana nufin cewa a yanzu duk wasu kadarorin shi kansa da kuma na wadannan kamfanoni dake karkashin ikon Amurka, an garkame su. Haka kuma ya zamo haramun ga duk wani Ba-Amurke yayi hulda da kamfanonin.

Daga shekarar 2000 zuwa yanzu, ma’aikatar harkokin kudi ta Amurka ta ayyana mutane 87 a matsayin manyan dillalan kwayoyi, ta kuma kafa takunkumi a kan kamfanoni da mutane fiye da 700.

XS
SM
MD
LG