Jami’an ‘yan sandan jihar Louisiana dake Amurka, sun bayyana mutumin nan da ya bude wuta jiya da yammacin Alhamis kan wata gidan nuna sinima ko majigi, inda ya kashe mutane biyu da jikata wasu bakwai, kafin ya harbe kansa har lahira.
Jami’an garin Lafayette sunce har yanzu suna neman karin bayani akan mutumin da ya bude wutar, mai suna Russel Houser ‘dan shekaru 59 da haihuwa. Shugaban ‘yan sandan garin Laffayette Jim Craft, ya bayyana shi a matsayin mai tabin hankali.
Kusan mutane 100 ne ke cikin wannan gidan sinima suna kallon fim mai suna Trainwreck, a lokacin da ‘dan bindigar ya fara harbin mutanen da suke kallon fim ‘din tare, da wata karamar bindiga.
Craft yace, da alamar mutumin yazo da shirin ya kashe mutane ne sannan ya gudu, amma isowar jami’an tsaro cikin gaggawa ne ya tilasta masa komawa cikin gidan siniman inda ya kashe kansa.
Har yanzu dai ba’a san dalilin da ya sashi yin haka ba.