Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Sayi Makamin Sindaran Nukiliya Daga Hanun Iran.


Sakatare harkokin wajen Amurka John Kerry,da Mohammad Javad Zarif, na Iran.

Ranar jumma'a, Amurka ta bada wannan tabbaci da ma'aikatun harkokin waje da makamashi suka bayyana.

Amurka zata sayi ton 32 na wani muhimmin sinadari da ake amfani da shi wajen kera makaman kare dangi daga kasar Iran, a wani yunkuri na taimkawa kasar, ta aiwatar da yarjejeniyar da manyan hukumomin duniya suka kulla da ita.

Jiya jumm'a, ma'aikatun harkokin waje da makamashi na Amurka, suka tabbatar da cewa Washington ta sayi na'urar da ake amfani da ita wajen sarrafa sindaran Plutonium daga Tehran.

An bada wannan sanarwar ce, a dai dai lokacinda Amurka da Iran, da jami'an wasu kasashe suka hallara a birnin Vienna, domin su tattauna kan aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla, kan shirin Nukiiyar Iran din.

Tunda farko Iran ta sayarwa Rasha sindaran Uranium wadanda ta karawa daraja.

An sami bayanan wannan cinikin ne, gabanin ganawar da aka shirya tsakanin sakataren harkokin wajen Amurka John kerry, da kuma takwaran aikinsa na Iran, Muhammad Javad Zariff, a gefen taron MDD, kan bikin sanya hanu kan yarjejeniyar da kasashen duniya suka kulla,gameda dumamar yanayi, a birnin New York.

XS
SM
MD
LG