Accessibility links

An Bada Buhu Dubu 390 Na Hatsi Ga Jihohin Dake Karkashin Dokar-Ta-Baci

  • Garba Suleiman

Wasu mata su na sayayya cikin kasuwa a Maiduguri, Jihar Borno.

Karamin ministan kudi, Dr. Yerima Ngama, yace shugaba Goodluck Jonathan ya kuma bayarda tufafi da kudi Naira miliyan 250 na agaji ga jihohin uku

Gwamnatin tarayyar Najeriya, zata raba agajin buhu dubu 390 na hatsi ga mutanen jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa, wadanda suke fuskantar karancin abinci a saboda dokar-ta-bacin da aka kafa musu da yadda wannan ya shafi noma a daminar bana.

Karamin ministan kudin Najeriya, Dr. Yerima Ngama, ya fadawa Umar Faruk Musa na Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa adadin abincin da zasu kai, zai kunshi motocin tirela har 650, kuma daga cikinsu, motoci 500 zasu dauki masara ne. Sauran kayan abincin da za a kai zasu hada da shinkafa, dawa, gero, gishiri da kuma man gyada.

Dr. Ngama yace rabin dukkan wadannan kayayyaki, za a bayar da su ne ga Jihar Borno, jihar da ta fi fama da ukubar yakin da ake yi da 'ya'yan kungiyar nan ta Boko Haram. Za a mika kashi 34 cikin 100 ga Jihar Yobe, yayin da sauran kashi 16 daga cikin 100 za a kai Jihar Adamawa.

Dr. Ngama yace sun kuma sayi atamfofi da shadda wadanda su ma za a raba ga mutanen jihohin uku.

Karamin ministan kudin na Najeriya, yayi dalla-dallar bayani ma wakilin Sashen Hausa, Umar Faruk Musa, game da wannan agaji kamar haka.

XS
SM
MD
LG