Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Al’umar Jihar Filato Dasu Rungumi Zaman Lafiya


Zaman lafiya a jihar Plateau

Wasu da ba’a tantance ba suka kashe mutane uku a wani kauye a karamar hukuymar Bassa.

Gwamnatin jihar Filato ta bukaci al’umar jihar dasu rungumi zaman lafiya bayan wasu hare hare da satar Shanu dake afkuwa a wasu sassan jihar cikin ‘yan kwanakinan.

Daraktan hulda da manema labarai da jama’a, a ofishin Gwamnan jihar Filato Emmanuel Nanlay, ya bayana takaicinsa kan sake barkewar rikici da ake samu a wasu kananan hukumomin jihar Filato.

Rikicin ya fara ne tun ranar litinin inda wasu da ba’a tantance ba suka kashe mutane uku a wani kauye a karamar hukuymar Bassa.

Shugaban kungiyar matasa ta Junde Jam, Alhaji Saidu Maikano, ya ce an sace masu Shanu fiye da dari,yana mai cewa muddin ba’a dena sace sacen Shanun da akeyi ba zaman lafiya nada wahala. Fulani sun dogara ga Allah sun dogara ga Shanun su.

Ya kuma yi kira ga shugaban Najeriya da jami’an tsaro da su duba halin da Fulani ke ciki a jihar Filato.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:03 0:00

XS
SM
MD
LG