Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ceto Wasu Yara Daga Hannun 'Yan Fashi


‘Yan Sanda sun samu nasarar ceto wasu yara biyu a hannnun wasu ‘yan fashi kuma masu satar mutane a Dandume dake cikin jahar Katsina a kokarin ceto yaran, daya daga cikin barayi ya rasa ransa.

Kwamishinan ‘yan sandan jahar ta Katsina, Alhaji Usman Abdullahi, wanda ya bayyana haka ga manema labarai ya ce ‘yan fashin sun yiwa garin Mahuta, duran mikiya ne akan Machina hudu ne.

Da ‘yan fashin suka shiga garin na Mahuta, sai suka nufi gidan wani Alhaji Rabiu Maidara, suka bukaci ya basu makudan kudi, da babu kudin ne suka yi awon gaba da ‘ya’yan sa su biyu.

Da samun rahoton sai jami’an ‘yan Sandan suka bazama inda Allah ya basu kwato yaran bayan da aka yi dauki ba dadi da ‘yan fashi , ‘yan Sandan sun samu bindiga AK47 da albarusai da kuma Adduna.

XS
SM
MD
LG