Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cimma Yarjejeniya Tsakanain Kasashen Sudan Biyu.


Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir Mayardit, daga hagu, da takwaransa Omar al-Bashir, a birnin Juba, na Sudan ta kudu.

Wakilai daga kasashen Sudan da Sudan ta kudu sunce shugabannin kasashen biyu zasu gana nan bada jumawa ba, yayinda sassan suke ci gaba da shawarwari kan shata kan iyaka da kuma rabon kudaden mai.

Wakilai daga kasashen Sudan da Sudan ta kudu sunce shugabannin kasashen biyu zasu gana nan bada jumawa ba, yayinda sassan suke ci gaba da shawarwari kan shata kan iyaka da kuma rabon kudaden mai.

Talata, a Addis Ababa fadar kasar Habasha, wakilan kasashen biyu sun amince zasu kafa kwamitoci da zasu kula da batutuwa masu sarkakiya da suka hada da tanatance wanene dan kasa, batun kan iyaka, batutuwa da suka zafafa zaman dar-dar tsakanin kasashen biyu.

Ana sa ran shugaba Omar l-Bashir na Sudan, da Silva Kiir na Sudan ta kudu zasu sanya hanu kan yarjejeniyar cikin makonni masu zuwa.

Cikin watan Yuli na bara ne Sudan ta kudu ta balle daga Sudan, duk da haka akwai sauran muhimman batutuwa da ba’a warware ba, kuma shawarwari da ake yi a Addis Ababa, da nufin shawo kan wadan nan matsalolin, da ahalin yanzu ya dauki kwanaki 10 yana tafiyar hawainiya.

Wakilin Muriyar Amurka a taron, yace daya daga cikin kwamitocin da za a kafa zai dauki nauyin cimma matsaya kan makomar mutane dubu dari bakwai ‘yan kudancin Sudan wadanda ahalin yanzu suke arewa, wadanda suka zama ‘yan kasashen waje bayanda kudancin kasar ta balle.

Haka kuma akwai dubban ‘yan arewa wadan d suke Sudan ta kudu. Tilas akwashe su nan da 8 ga watan Afrilu, idan ba an cimma wata yarjejeniya ba.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG