Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cire Najeriya


Magoya bayan Super Eagles na Najeriya

'Yan wasan Super Eagles na Najeriya sun buga kwallo sosai a wasansu na karshe a rukuni na biyu, suka yi kunnen-doki da Koriya ta Kudu, amma kuma za su koma gida yayin da Koriya zata shige

An yi waje-rod da 'yan wasan Super Eagles na Najeriya daga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya ta 2010 da ake yi a Afirka ta Kudu, a bayan da suka yi kunnen-doki da ci biyu da biyu da 'yan wasan kasar Koriya ta Kudu. Duk da haka, Koriya ta Kudu zata shige zuwa zagaye na gaba, a bayan da Ajantina ta doke Girka da ci biyu da babu a daya wasan na rukunin "B".

Najeriya ta shiga wannan wasa tana neman ta doke Koriya ta Kudu, tana kuma fatar Ajantina ta doke Girka. Ajantina dai ta doke Girka, amma Najeriya ta kasa lashe wasanta da Koriya ta Kudu.

'Yan wasan Najeriya suka fara jefa kwallo ta kafar Kalu Uche, amma sai Koriya ta Kudu ta rama daga baya. Ana komowa daga hutun rabin lokaci Koriya ta Kudu ta kara jefa kwallo na biyu. najeriya ta rama wannan ta bugun fenariti, amma tun daga nan ta yi ta kai kora, kwallo na kwace mata.

Ya zuwa yanzu dai, dukkan kasashen Afirka da suka kammala wasanninsu na zagayen farko ba za su samu hayewa ba, a bayan da aka cire Afirka ta Kudu mai masaukin baki.

Sauran kasashen Afirka da suka rage cikin wannan wasa sune Aljeriya da Ghana da Ivory Coast (Cote D'Ivoire) da kuma Kamaru.

XS
SM
MD
LG