Mai rikon mukamin shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya umurci shugaban hukumar zaben kasar da ya sauka daga kan wannan kujera, a bayan da ka ayi ta nuna damuwar cewa ba zai shirya zaben gaskiya a shekara mai zuwa ba.
A cikin wata sanarwa da ya bayar jiya laraba, Mr. Jonathan ya ce an tura Maurice Iwu, shugaban hukumar zaben da ake kira INEC a takaice, zuwa hutu nan take. Har yanzu ba a bayyana wanda zai gaje shi ba tukuna.
A watan da ya shige, daruruwan mutane sun yi zanga-zanga a kofar hukumar zaben a Abuja su na neman da a cire Mr. Iwu. Ita ma Amurka ta bukaci da a cire shugaban hukumar zaben.
Maurice Iwu shi ne ya shirya zaben 2007 wanda ya dora shugaba Umaru Musa 'Yar'aduwa da mataimakinsa Goodluck Jonathan a kan karagar mulki. Akasarin 'yan kallo sun ce an tabka magudi tare da cin zarafin abokan hamayya a lokacin wannan zabe na 2007.
Za a gudanar da zaben shugaban kasa na gaba a Najeriya a watan Afrilun 2011.