Accessibility links

An fara samun zaman lafiya a kasashen Musulmi bayan zanga zanga ta tsawon kwanaki


Masu zanga zanga a birnin Alkahira
Kura ta fara lafawa a kasashen Musulmi bayan shafe kwanaki ana zanga zanga da tashin hankali a wadansu lokuta, dangane da silman batancin da aka yayata a na’urar internet.

Ma’aikatan kashe gobara a Misira sun kashe wuta da aka cinna a dandalin Tahrir da ta sa hayaki ya turnuke sararin sama. Ma’aikatan kwana kwanan sun kashe wuta da aka cinna a wurare dabam dabam bayan an kwana ana fito mu gama tsakanin masu zanga zanga da ‘yan sanda, da ya yi sanadin kashe wani mai zanga zanga guda.

A Sudan inda aka gudanar da zanga zangar da tayi sanadin rasa rayuka, ‘yan sanda sun yi ta sintiri a titunan Khartoum jiya asabar yayinda ake ci gaba da ganin alamun barna a titunan da ofisoshin jakadancin Birtaniya da kuma Jamus suke.

Sauran kasashen da aka shafe kwanaki ana zanga zanga da suka hada da Tunisiya da Yemen suma sun wayi gari yau lafiya, sai dai an ci gaba da wata sabuwar zanga zanga yau a Afghanistan da India da Sydney da kuma Australia.

A kalla masu zanga zanga biyar ne suka mutu cikin wannan makon, da suka hada da Tunisiyawa biyu da wani dan kasar Lebanon daya da kuma a kalla mutum guda dan kasar Sudan.
XS
SM
MD
LG