Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Zanga-zanga Kan Alkawurorin Zaben Da Trump Yayi Lokacin Kamfen.


Wasu masu zanga zangar nuna adawar zaben Donald Trump shugaban Amurka.
Wasu masu zanga zangar nuna adawar zaben Donald Trump shugaban Amurka.

Masu rajin kare 'yancin Bil'Adama da tsiraru sun yi gangami jiya Asabar a Washington DC.

Mako daya gabannin a rantasar da sabon shugaban Amurka Donald Trump, an fara zanga zanga kan alkawurori daban daban da yayi lokacin yakin neman zabe.

Wani gangami mai suna "We shall not be Moved" yana karkashin jagorancin dan gwagwarmyar nan Rev. Al-Sharpton.

Kungiyar ta fada a shafinta a internet cewa "kare 'yancin 'yan kasa, 'yancin yin zabe ga mutane da aka yi watsi da su, samarda inshoran kiwon lafiya ga Amurkawa baki daya, da kuma baiwa kowa 'yanci ba tareda nuna fifiko, sun dara ko wani irin zazzafar muhawara da zamu fada ciki,". Kungiyar ta ci gaba da cewa "kungiyoyi sun yi zamaninsu sun wuce, zabe yana zuwa ya wuce, amma tilas akwai abunda zai dore, kuma ba za'a yi jayayya ko kawar da shi ba".

Ana wadannan maci-macin ne a karshen makon da ake hutu gobe litinin, domin karrama gwarzon yaki da wariyar launin fata Dr. Martin Luther King, wanda ya shahara saboda rashin gajiyawa a yaki domin kawo karshen wariyar launin fata, da karfafa 'yancin tsiraru, wand a yayi a tsakankanin shekarun 1950-da 60.

A can maraicen jiya Asabar anan Washington, magoya bayan bakin haure da 'yancin tsiraru, wadanda su kira kansu "Here to stay" da turanci, sun gudanar da zanga a harabar wani coci.

"Tawagar Trump tuni tayi shelar cewa, cikin matakn farko da zata dauka shione auna bakin haure da musulmi," kalaman da gangamin ya rubuta a shafinsa ainternet.

XS
SM
MD
LG