Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Goce Da Wani Sabon Fada A Mali : Sojojin Cadi 13 Dana Mayakan Sakai 65 Sun Mutu.


Sojojin Mali suke bude wuta kan maboyar mayakan sakai a Gao.
A Mali an goce da sabbin fadace-fadace a sassa biyu na arewacin kasar inda sojojin Faransa da wasu kasashen Afirka suke dafawa dakarun Mali, a fafatawar da suke yi na tusa keyar mayakan sakai ‘yan gani-gashenin Islama.

Wakilin Muriyar Amurka na Sashen Faransa yace kungiyar ‘yan tawayen abzinawa mai lakanin MNLA tana fafatawa yau Asabar da wata kungiyar mayakan sakai da ba'a bayyana sunanta ba, kusa da wani gari da ake kira Tessalit.

A jiya jumma’a wani bam da aka boye cikin wata mota ya tashi a harabar kungiyar ‘yan tawayen abzinawa kusa da garin Tessalit, ya kashe mutane biyar, ciki har da mutane biyu da ake zargin sune ‘yan harin kunar bakin waken.

Ahalinda ake ciki kuma, shugaban Faransa, Francois Hollande yace dakarun kasarsa da na Cadi suna gwabza fada da mayakan sakai a yankin Ifoghas mai tsaunuka kusa da kan iyakar kasar da Aljeriya. Mr. Hollande ya fadawa manema labarai yau Asabar cewa dakarun sun hakikance cewa gungun hadakar ‘yan ta’adda suna neman mafaka cikin tsaunukan.

A jiyan rundunar sojojin Cadi daga cadin ta fada cewa an kashe mata sojoji 13, a kuma kashe ‘yan gani kashenin Islama su 65 a wani kazamain fada da aka gwabza a yankin Ifoghas din.
Cadi tana da sojoji dubu daya da dari shida a Mali.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG