Accessibility links

Hukumar agaji ta Najeriya ta horar da 'yan jarida game da yadda zasu sanarda da mutane da fadakar da ilimantar da su game da kowane bala'i

Hukumar agaji ta Najeriya ta horar da 'yan jarida da ma wadanda suka sadakar da kansu domin su yi taimako dangane da yadda zasu sanarda da mutane da fadakar da ilimantar da su game da kowane bala'i.

A wani mataki na yadda kafofin labarai zasu fadakar da jama'a su kuma ilimantar da jama'a dangane da kowane irin bala'i hukumar dake samarda taimakon gaggawa dake arewa maso gabashin Najeriya mai ofishinta a garin Gombe ta shirya shirin horar da 'yan jarida a garin Bauchi da kuma wadanda suka bada kansu domin taimakawa idan wani bala'i ya auku.

Mr Dadirep jami'in aiki na hukumar ya kara haske a kan shirin. Ya ce suna horar da wadanda suka bada kansu su yi taimako domin yin shirin ko ta kwana ganin yadda hadaruruka ke yawan faruwa a kasar kamar ambaliyar ruwa, gobara da wasu makamantansu. Ya ce canji yanayi da ake samu ya sa abubuwa suna faruwa. Misali a shekarar da ta gabata jihohi ashirin da uku suka samu ambaliyar ruwa lamarin da bai taba faruwa a kasar ba. Masana sun sake fada cewa ambaliyar ruwa da za'a samu a wannan shekarar zai fi na bara. Don haka wajibi ne a horar da mutane su kuma su taimaka su horar da wasu domin a samu cikakken taimako.

Mohammed Inuwa Bello jami'in jihar Bauchi mai kula da agajin gaggawa ya ce gini kan hanyar ruwa na cikin dalilan dake haddasa ambaliyar ruw da kuma rubar da shara. Ya ce sun zagaya sun fadakar da mutane su guje ma yin hakan.

Ga rahoton Abdulwahab Mohammed.

XS
SM
MD
LG