Babban jami’in ‘yan sanda Moses Ombati yace ya hakikanta cewa, wadanda suke goyon bayan kungiyar mayaka ta al-Shabab a Somalia suke da alhakin harin.
Ranar Jumma’a dakarun kasar Kenya suka yi kazamin gumurzu da kungiyar al-Shabab ta Somaliya a Kismayo dake tashar jirgin ruwa, suka tilasa mayaka kauracewa wuri na karshe da suke iko a kai.
Yan sanda sun ce yaran suna ajin Sunday sukul ne a majami’ar St Polycarp dake birnin Nairobi, lokacin da wani ya jefa gurneti a ciki.