Accessibility links

An kai hari kan majami'ar St John's a garin Bauchi


Motar da dan kunar bakin wake ya yi amfani da ita wajen kai hari kan majami'ar St. John's Catholic a Bauchi,
Rundunar ‘yan sandan Najeriya tace, wani dan kunar bakin wake ya kashe a kalla mutane biyu ya kuma raunata sama da arba’in da biyar a wata majami’a dake garin Bauchi a arewacin Najeriya.

An kai harin ne yau lahadi da safe a majami’ar St John’s dake cikin garin Bauchi, babban birnin jihar.

Kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin harin. Kungiyar nan mai tsats-tsauran ra’ayin addini da aka fi sani da suna Boko Haram ta dauki alhakin irin wadannan hare haren da aka kai a lokutan baya a arewacin kasar.

Kungiyar tace, tana tada kayar baya ne da nufin ganin an kafa shari’ar Musulunci a duk fadin Najeriya, kasar da tafi kowacce yawan al’umma a nahiyar Afrika.
Kungiyar bata amince da gwamnatin Najeriya ko tsarin mulkin kasar ba.
XS
SM
MD
LG