Bom-bomai uku sun tashe a wurare uku masu muhimmanci a birnin Al-kahira yau Juma'a, a ciki harda dan harin kunar bakin wake wanda ya kaiwa shekwatar ofishin 'yan sandan kasar hari, har hakan yayi sanadiyar rayukan mutane, a mummunnan hari na farko akan babban birnin kasar, lokacin da mayakan sa kai suke tada tarzoma bayan hambarar da shugaba Mohammed Morsi da sojojin kasar suka yi.