Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Turkiyya An Kama Kusan Mutane Dubu Daya Masu Zanga Zanga A Duk Fadin Kasar


'Yansandan kwantarda tarzoma sun yi amfani da borkonon tsohuwa wajen tarwtsa masu zanga zanga.

Mutane masu yawa ne a biranen Ankara da Istanbul na turkiyya suka cigaba da zanga zanag har cikin daren jiya Asabar a lamari da yama zanga zanga a fadin kasar baki daya na nuna kyamar gwamnati.

Mutane masu yawa ne a biranen Ankara da Istanbul na turkiyya suka cigaba da zanga zanag har cikin daren jiya Asabar a lamari da yama zanga zanga a fadin kasar baki daya na nuna kyamar gwamnati.

Wuta tana ci kan titunan birnin Ankara da Istanbul, yayinda hayakin borkonon tsohuwa da hayakin wuta da suke ci sun turnuke sararin samaniya.

Abunda ya fara daga zaman durshen na nuna rashin amincewa da shirin kawata babban dandalin dake birnin Istanbul, yanzu ya rikida ya zama yamutsi inda dubban jama’a suka fantsama kan tituna domin zanga zanga nuna kin jinin gwamnati.

PM Erdogan yayi alwashin zai cigaba da aikin sabunta dandalin, daga nan yayi kira ga mutanen d a suke zanga suk tsaida shih aka.

Zanga zangar ta bazu zuwa wasu biranen inda mutane suke Allah wadai da abunda suke kallo gwamnatin kasar ta Mr. Erdogan a matsayin ‘yar kama kariya.

Ministan harkoki cikin gida na kasar Muammar Guler yace an kama fiyeda mutane dari tara a zanga zangogi da aka gudanar a duk fadin kasar, yayinda aka jikkata ‘Yansanda 26, farar hula 53 kuma suka sami raunuka. Tuni aka bada rahoton sakin wasu daga cikin wadanda aka kama

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG