Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kammala Taron Kwana Uku Na Baje Kolin Kayan Jiragen Sama a Accra, Ghana


Taron baza kolin jiragen sama da kayayyakinsa a Accra Ghna

An kwashe kwanaki uku ana baje kolin kayan jiragen sama daga sassan da kamfanoni a babban Birnin Ghana wato Accra inda shugaban Ghana din ya yi alkawari daukan matakan habaka balaguron jiragen sama tsakanin al’ummominsu

An kammala taron kwana uku na baza kolin kayan jiragen sama da abubuwan dake da alaka da jiragen sama a nahiyar Afirka.

Kamfanoni dake kera abubuwa daban daban suka nuna sha’awar yin kawance da kasar Ghana akan alkawarin Shugaban kasar na maida kasar ta zama jigo a harkokin jiragen sama a yammacin Afirka.

Shugaban Ghana din, Nana Akufo-Addo, ya nemi shugabannin kasashen yammacin Afirka su maida hankali wurin zartad da kudurin Yamoussoukro na 1988 inda shugabannin suka amince da samar da walwalar aikin jiragen sama tsakaninsu.

Captain Bala Jibrin, babban jami’in wani kamfanin gina filayen jiragen sama mai zaman kansa daga Najeriya ya bayyanawa wakilin Muryar Amurka Ribwan Abbas cewa zirga-zirgan jiragen sama cikin kasashen Afirka kashi 15 ne kawai. Wato ‘yan Afirka suna zirga zirgansu na kashi 85 da kasashen Turai da Asiya ne. Yace dole ne a kaiwa Kungiyar Hadin Kan Kasashen Afirka da hedkwatarta ke a birnin Addis Ababa na Ethiopia bukatar karfafa karatu, wasanni, kasuwanci, da zumunci tsakanin kasashen Afirka.

Ga rahoton Ribwan Abbas da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:21 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG