Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kara Kamun Wasu Manyan Jami'an Hukumar FIFA


Sakataren Hukumar FIFA Jerome Valcke

An fadada binciken abun fallasan nan da hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta duniya FIFA take fuskanta.

Jiya Alhamis ma'aikatar harkokin shari'a ta Amurka ta bayyana sunayen karin jami'ai 16 na hukumar FIFAn,wadanda ake zargi da laiuffukan aikata rashin gaskiya daban daban. Da wadannan sabbin tuhuma da jami'an Amurka suka bayyana shine ya kawo adadin mutane da kdarori da ake zargi zuwa 41.

Cikin sabbin wadanda ake zargi harda manyan jami'an hukumar biyar wadanda har yanzu suke bakin aiki, wadansu kuma sun bari. Ciki harda wasu wadanda suke lura da shiyyoyi kamar a kasashen da suke arewacin nahiyar Amurka da wadanda suke tsakiya da kuma yankin Caribbean, da kuma hukumar kula da harkkin kwallo dake kudancin nahiyar.

Ma'aikatar ta shari'an ta kuma yi bayanin cewa tuni aka sami mutane 12 da kamfanoni biyu wadanda suke hajar kayayyakin wasan kwallon kafa tuni aka samesu da laifi sakamkon binciken da ake ci gaba da yi kan wannan batu,wadannan mutane da kamfanonin sun amincce zasu maido da kudi dala milyan 190. Haka nan kuma an yi talala ga kudade sama da dalar Amurka milyan dari anan cikin gidan Amurka da kuma kaetare dangane da wadannan laifuffuka.

XS
SM
MD
LG