Accessibility links

An Harbe Aka Kashe 'Yan Zanga-Zanga Uku A Masar.


Magoya bayan shugaba Morsi, da masu adawa suka baiwa hamata iska a harabar fadar shugaban kasa a Alkahira, ranar laraba.
An harbe aka kashe akalla masu zanga- zanga uku a Alkahira, babban birnin kasar Masar jiya laraba, a wasu rangamomi tsakanin magoya da masu adawa da shugaba Mohammed Morsi.An cigaba da tarzomar har zuwa safiyar yau Alhamis. Akwai rahotanni da suke cewa fiye da mutane 300 kuma sun jikkata.

Rahotanni daga inda ake rikicin daga wakiliyar Muriyar Amurka, ta ce sabon tarzomar ta barkene lokacinda magoya bayan Mr. Morsi masu ra’ayin islama, suka kai hari kan masu zanga-zangar nuna adawa kan abunda suka kira babakere kan madafun iko da shugaba Morsi yayi.

Arangamar da aka yi a sansanin fadar shugaban kasar, itace irinta ta farko da ‘yan hamayya a kasar wacce ta rabu gida biyu kan ra’ayin siyasa suka baiwa hamata iska, tun zanga zangar bara wacce ta tilastawa tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak yin murabus.

A gefe daya kuma, wasu hadiman shugaba Morsi uku sun bada sanarwar yin murabus, domin bayyana rashin amincewarsu kan dokar shugaban kasar wacce ta bashi dumbin iko. Biyar daga cikin masu baiwa shugaban kasar shawara 17, sun yi murabus daga 22 ga watan jiya.
XS
SM
MD
LG