Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FILATO: An Kashe Mutane 23 a Harin Kadarko


Ire-iren harin da ake kaiwa jama'a

Rahotanni sun nuna cewa wasu sojoji sun dira a garin Kadarko a jihar Filato suka kuma kashe mutane akalla guda 23 kamar yadda wani sheda ya bayyanawa wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji.

Kisan da ake sa ran ramuwar gayya ce game da wasu sojoji guda 6 da aka kashe a garin tare da yanke wasu sassan jikinsu. An ce sojojin da suka kai harin har da kona gidajen jama’a har da na sarkin garin.

Muryar Amurka ta tuntubi kakaki rundunar sojojin bada tsaro Kaftin Ikedichi inda ya shaida mata cewa su sojojinsu basu kaiwa kowa hari ba, hasali ma dai sai bawa mutanen kauyen kariya da suke yi a ko yaushe.

Game da mutanen da aka ce an kashe a kauye jami’in sojan ya bayyana cewa suna nan suna bincike da zarar sun gano abin da ya faru zasu sanar da jama’a.

Dama mutanen garin na zargin cewa wasu mahara da sukan kai samame ne suka kashe jami’an tsaron. Saboda haka suke zaton cewa ‘yan ta’addar ne suka kashe sojojin da ake zargin an kashe.

FILATO An Kashe Mutane 23 a Harin Kadarko - 3'25"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG