Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe mutane biyu a wani hari da aka kai a birnin New York


ma'aikatan ceton rayuka a wurinda aka yi harbi
ma'aikatan ceton rayuka a wurinda aka yi harbi
Rahotanni na nuni da cewa, an kori dan bindigan nan da ya yi harbi ya kashe wani tsohon abokin aikinsa a wani dogon gini a birnin NY da ake kira Empire State Building daga aiki, wanda ‘yan sanda suka kashe bayan ya harbe tsohon abokin aikin nasa.

Kwamishinan ‘yan sanda na birnin NY Ray Kelly ya shaidawa manema labarai cewa, an kori dan bindigar, dan shekaru 53 Jeffrey Johnson daga wani kamanin kayan addon mata dake kusa da ginin kusan shekara daya da ta shige, ya kuma bayyana cewa, dan bindigar ya harbi tsohon abokin aikinsa dan shekaru 41 da bindigar hannu a ka.

Kwamishinan ‘yan sanda Kelly ya bayyana cewa, Johnson ya yi kokarin gudu amma wani mutum dake aikin gini a wurin ya sanar da wadansu ‘yan sanda biyu wadanda suka bi dan bindigar suka bude mashi wuta suka kuma kashe shi bayanda ya auna bindiga kansu.

Babban jami’in ‘yan sandan da magajin garin birnin NY Micheal Bloomberg sun ce an yiwa mutane tara-maza bakwai mata biyu rauni yayin musayar wutar, suka kuma bayyana cewa, yana yiwuwa an jiwa wadansu mutane rauni a cikin kuskure lokacin da ‘yan sanda suke musayar wuta da dan bindigan. Bisa ga cewarshi, babu wanda yaji mummunan rauni.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG