Accessibility links

An kashe mutane hudu a kasar Kenya

  • Jummai Ali

Majinyatta da suka jikatta kwance a asibiti a Kenya

Mutane hudu sun muta a sakamakon harin gurnati a Kenya

Wani harin gurnati da aka kai Nairobi, baban birnin kasar Kenya ya kashe akalla mutane hudu da raunana kimamin mutane arba’in.

Jami’ai sunce fashe fashe na jiya asabar su faru ne a sakamakon gurnatin da aka jefa akan wani wurin shiga mota. Mukadashin mai magana da yawun rundunar yan sandan kasar, Charles Owino ya ambaci shedun gani da ido na cewa an jefo gurnati ne daga wata motar dake wucewa.

Yace shedun gani da ido su gaya musu cewa, kila wasu mutane dake cikin wata mota wadda take wucewa ne suka jefo gurnatin cikin taron mutane a wurin shiga motar. Wannan ne hari na baya bayan nan cikin jerin hare haren da ake kaiwa Nairobi tun lokacinda kasar Kenya ta tura sojojinta zuwa Somaliya a watan okotoba domin fafatawa da yan yakin sa kan kungiyar Al Shabab wadda take da alaka da kungiyar Al Qaida.

Jim kadan bayan harin, yan sanda suka kama wani mutum wanda yayi ikirarin cewa shi dan kungiyar Al Shabab ne.

XS
SM
MD
LG