Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kori Karin Ma'aikata Dubu UKu Da Dari Shidda A Afrika Ta Kudu


Ma'iaktan hakar mu'adinai a kofar ofishin jakadancin Birtaniya
Ma'iaktan hakar mu'adinai a kofar ofishin jakadancin Birtaniya
Kimanin ma’aikatan hakar mu’adinai dubu uku da dari shida aka kora jiya Talata yayinda kungiyar kwadago take ci gaba da tada kayar baya a kamfanonin hakar mu’addanan kasar.

Kamfanin hakar mu’adanai na Atlatsa Resources yace ya salami ma’aikata dubu biyu da dari daya da sittin, wadanda suka shiga yakin aiki tun ranar daya ga wannan wata na Oktoba, a kamfanin karafanta na Bokoni. Kamfanin ya bayyana cewa, ma’aikatan suna da zuwa karshen wunin yau Laraba su daukaka kara.

Tun farko kamfanin Gold One International ya sanar da korar sama da ma’aikata dubu daya da dari hudu a ma’aikatarsa ta Ezulwini dake kudu maso yammacin birnin Jonnesburg. Ma’aikatan kamfanin ma sun shiga yajin aiki ranar daya ga watan Oktoba.

Kotunan Afirka ta Kudu sun ce dukan yajin aikin sun sabawa doka.

Ranar Jumma’a kamfanin hakar karafa na Anglo American ya kori ma’aikata dubu goma sha biyu daga ma’aikatarsa ta Rustenberg bayan sun shafe makonni uku suna yajin aiki.

Yajin aikin ya biyo bayan tashin hankali da aka yi, yayin wani yajin aiki a ma’aikatar hakar karafa ta Lonmin dake garin Marikana. Arangamar da aka yi a wurin da ta hada da harbe-harben da ‘yan sanda suka yi, ta yi sanadin kashe mutane 46, sai dai daga baya ma’aikatan sun sami karin kashi 20% na albashi.

Ma’aikata a wadansu kamfanonin hakar mu’adinai suna neman a yi masu irin wannan karin albashin.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG