Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nada Adeyeye a Matsayin Sabon Sarkin Ife


Engineer Rauf Aregbesola is Osun State governor

Rahotanni daga jahar Osun da ke kudancin Najeriya na cewa an nada Prince Adeyeye Ogunwusi a matsayin sabon Sarkin Ife.

Mai baiwa gwamnan Jahar shawara kan harkokin da suka shafi ‘yan Arewa mazauna garin, Imam Bashir Hussain, ya tabbatarwa wakilin Muryar Amurka Hassan Umaru Tambuwal da sabon nadin da aka yi.

“Wanda aka fitar shine Prince Adeyeye Ogunwusi wanda ya fito daga Gidan Geisi, daga cikin matakan da aka duba wajen zabensa, su ne na farko matashi ne, na biyu yana da basira yana kuma da kyakyawar mu’amulla da mutane da kuma biyayya da hakuri.” In ji Hussain.

A cewar Hussain, gwamnan Jahar Rauf Aregebsola ne ya tabbatar da zabin sabon sarki Adeyeye ta hanu mai bashi shawara kan harkokin hulda da jama'a.

A watan Yulin da ya gabata, tsohon sarki Okunade Sijuwade ya rasu, yana mai shekaru 85, bayan da ya yi wata ‘yar gajeruwar rashin lafiya da ta sa aka kai shi London.

An samu takaddama game da wanda zai maye gurbin na sa saboda gidajen saurata da dama da sun nuna sha’awarsu ta hawa kujerar.

Masauratar ta Ife it ace masaurata mafi girma da kabilar Yarbawa suka fi girmamawa a Najeriye, wacce ke jahar Osun a kudu maso yammacin kasar.

Ga karin bayani game da nadin a wannan rahoto da Hassan Umaru Tambuwal ya aiko mana:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG