Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sace Sarkin Bukuyyum A Jihar Zamfara


Gwamna Abdul'aziz Abubakar Yari na Jihar Zamfara, arewa maso yammacin Najeriya.

Rahotanni daga jihar Zamfara na nuni da cewa, wadansu ‘yan bidiga da ba a san ko su wanene ba sun sace sarkin Bukuyyum dake shelkwatar KRH.

Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya auku ne da daren jiya jumma’a, sa’adda sarkin na Bukuyyum alh Mohammadu Usman yake zaman jiran sallar Isha a harabar wajen fadarsa dake garin na Bukuyum hedkwatar karamar hukumar ta Bukuyun dake jihar Zamfara.

Kwamishinan watsa labarai na jihar Zamfara alhaji Mohammed Ibrahim birnin magaji ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya bayyana cewa, ‘yan bindigar sun afkawa basaraken ba shiri suka kwace wayoyinsa na salula suka tilasa shi shiga cikin wata mota da suka zo da ita kana suka tafi suna harbin iska domin razana wanda zai nemi binsu.

Kawo yanzu dai babu wani karin haske dangane da maharani ko kuma inda suka tafi da shi, yayinda kwamishin yace jami’an tsaro sun shiga bincike.

Ga Rahoton da wakilin Sashen Hausa Murtala Faruk Sanyinna ya aiko:

Rahoton Sace Sarkin Bukkuyum-2:27
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Shiga Kai Tsaye

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG