Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Koma-Baya A Kokarin Hana Kwararar Mai A Cikin Tekun Mexico


Jami'an kamfanin mai na BP sun ce an samu koma-baya a kokarin da ake yi na saukar da wani rumbu a bakin rijiyar mai dake kwarara cikin teku domin hana man yoyo.

Jami'an kamfanin mai na BP sun ce an samu koma-baya asabar din nan a kokarin da kamfanin yake yi na hana tsiyayar mai daga wata rijiyar dake karkashin teku ta hanyar saukar da wani rumbun kankare a daidai bakin rijiyar dake tuttudo da danyen man.

Kamfanin BP yace wani abu mai kamar gudajin kankara yayi ta fitowa yana mannewa a cikin wannan rumbu a lokacin da aka yi kokarin saukar da shi a bakin rijiyar, dake wuri mai zurfin kilomita daya da rabi a can karkashin tekun Mexico.

Jami'ai suka ce wannan abu mai kamar kankara, gauraye ne na wani ruwan magani dake mannewa jikin ruwa yana daskarar da shi, kuma yana iya kamawa da wuta. Kamfanin na BP yace yana nazarin yadda zai shawo kan wannan sabuwar matsala.

A yayin da ma'aikata ke kokarin rufe bakin wannan rijiya dake yoyon mai a cikin teku, ma'aikatan da suka kubuta da rayukansu a lokacin da dandalin hako mai daga wannan rijiya yayi bindiga ya kuma nutse a cikin teku, sun ce da alamun iskar gas ta Methane da ta biyo cikin bututu ta yiwo sama daga wannan rijiya ita ce ta kama da wuta ta yi bindiga a lokacin da ta iso saman teku inda wannan dandalin hakar mai yake.

Ma'aikatan na kamfanin BP suka ce da alamun kyastun wuta daga injunan lantarki na tono mai dake kan dandalin shi ne ya sa iskar gas din ta Methane ta kama da wuta.

XS
SM
MD
LG